Gwamnatin Kaduna Ta Warware Rikicin Filin Makarantar Jama’atu a Zariya
Gwamnatin Jihar Kaduna ta warware rikicin mallakar filin makarantar Jama’atu School of Health Technology, Kofar Kibo, Zariya, bayan ta bayar da takardar mallakar fili (Certificate of Occupancy – C of O) ga Jama’atu Nasril Islam (JNI) Zaria ƙarƙashin Masarautar Zazzau.
Takardar mallakar filin wadda Hukumar Kaduna State Geographical Information Services (KADGIS) ta bayar, ta tabbatar da cewa filin makarantar mallakin Masarautar Zazzau ne.
A yau da safe, Sheikh Makari Sa’idu ya jagoranci tawaga daga Hukumar Gudanarwar makarantar domin miƙa takardar ga Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmad Nuhu Bamalli, CFR, a fadarsa.
Sai dai an tattaro cewa kafin fitar da wannan takarda a hukumance, wasu mutane da ake zargin suna karkashin tasirin wasu tsoffin shugabannin Jama’atu Nasril Islam, tare da wasu da aka kora daga makarantar Jama’atu School of Health Technology, sun yi yunƙurin karɓar takardar daga KADGIS.
Duk da ƙoƙarin da Sarkin Zazzau, Malam Ahmad Nuhu Bamalli, ke yi na gyara da tsabtace harkokin tafiyar da makarantun Jama’atu Nasril Islam, ana zargin waɗannan mutane na ci gaba da kawo cikas ta hanyar shigar da kararraki a kotu domin dakile duk wani ci gaba da ake son samu.
Haka kuma, an dade ana zargin waɗannan mutane da aikata damfara, ciki har da karɓar kuɗaɗe daga ɗalibai waɗanda daga ƙarshe ba su samu damar kammala karatunsu a makarantar ba.
A cikin wata sanarwa, Sakataren Jama’atu Nasril Islam na Masarautar Zazzau, Alhaji Sa'idu Dogara, ya bayyana godiya ga Gwamnatin Jihar Kaduna da kuma Sarkin Zazzau bisa jajircewarsu da tsayin daka wajen ganin an warware wannan lamari.
Ya bayyana wannan nasara a matsayin babban mataki da zai kawo kwanciyar hankali, sahihanci da kuma ci gaban harkokin ilimi a makarantar.
Comments
Post a Comment