Sanata Kabiru Marafa ya fice daga jam’iyyar APC ya faɗa ta ADC
Tsohon Sanatan Zamfara-ta-Tsakiya, Kabiru Marafa, ya sanar da sauya sheƙarsa zuwa jam’iyyar ADC, inda ya zargi jam’iyyar APC da makarkashiya.
Sauyin sheƙar tasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da rikici a cikin jam’iyyar ADC, wanda ya kai ga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) kin amincewa da shugabannin bangarorin jam’iyyar, bayan hukuncin da Kotun Daukaka Ƙara ta yanke a ranar 12 ga Maris.
Jaridar TheCable ta rawaito cewa a cikin wata sanarwa da Mansur Haruna, Darakta-Janar na sabuwar kungiyar yaɗa labaransa ya fitar a yau Alhamis, Marafa ya ce sauyin jam’iyyar da ya yi wani babban mataki ne a tarihin siyasar jihar Zamfara.
Ya kuma bayyana cewa magoya bayansa da tsarin siyasar da yake da shi sun biyo shi zuwa sabuwar jam’iyyar.
Tsohon dan majalisar dattawan ya ce matakin ya biyo bayan taron manyan masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Kaduna, inda ya tattauna sosai da abokan siyasa da kuma magoya bayansa.
Ya ƙara da cewa nan gaba kadan za a gudanar da babban taron magoya bayan ADC a Gusau, babban birnin jihar Zamfara.
Marafa ya kuma soki gwamnatin da ke kan mulki, yana mai cewa tana kokarin haifar da rudani da rikice-rikice a cikin jam’iyyun adawa.
A watan Agustan na shekarar 2025, Marafa ya fice daga jam’iyyar APC, inda ya zargi Shugaba Bola Tinubu da yin watsi da jihar Zamfara duk da rawar da ta taka wajen nasararsa a zaben shugaban ƙasa.
Comments
Post a Comment