Shugaban majalisar dokoki na jihar Kebbi ya rasu
Shugaban majalisar dokokin jihar Kebbi, Muhammad Usman Zuru, ya rasu.
Rahotanni sun bayyana cewa ya mutu ne a wani asibiti da ke ƙasar Masar, inda yake karɓar magani kan wata cuta da ba a bayyana ba. An ce marigayin ya shafe wani lokaci yana fama da rashin lafiya kafin rasuwarsa.
Wata majiya daga gwamnatin jihar a Birnin Kebbi ta ce an kai shi ƙasar waje domin jinya ne bayan da yanayin lafiyarsa ya tsananta kafin fara azumin watan Ramadan da ya gabata.
Marigayin ya wakilci mazabar Zuru a Majalisar Dokokin jihar.
Wani mai taimaka wa gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, kan harkokin sadarwa da dabaru, Idris Abdullahi Zuru, ya bayyana rasuwar a matsayin abin firgici.
Ya ce, “Rasuwar Shugaban Majalisa, Rt. Hon. Muhammad Usman Zuru, ta zo mana a matsayin babban abin girgiza. Babban rashi ne ba ga Jihar Kebbi kaɗai ba, har ma da ƙasa baki ɗaya.”
Ya ƙara da cewa har yanzu gwamnati na tattara cikakken bayani kan yadda rasuwar ta faru, tare da cewa za a fitar da sanarwa a hukumance da kuma shirye-shiryen jana’iza bayan tuntubar iyalansa.
Comments
Post a Comment