Tinubu ya rantsar da Muttaqha Darma a matsayin ministan gidaje
Tinubu ya rantsar da Muttaqha Darma a matsayin ministan gidaje
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da Dr. Muttaqha Rabe Darma a matsayin Ministan Gidaje da Raya Birane, bayan amincewar majalisar dattawa.
Darma ya maye gurbin Ahmed Musa Dangiwa da ya yi murabus kwanan nan.
A wajen bikin rantsarwar da aka gudanar a fadar gwamnati da ke Abuja, Tinubu ya bayyana cewa nadin ya zo ne a wani muhimmin lokaci na ci gaban ƙasa, yana mai jaddada cewa ana buƙatar ƙwararrun mutane domin tafiyar da harkokin gwamnati.
Sabon ministan ƙwararre ne a fannin gudanarwa da ci gaba, inda ya yi karatu a Jami'ar Bayero Kano da kuma wasu jami’o’i na ƙasashen waje. Ya taɓa riƙe mukamai da dama a jihar Katsina, ciki har da kwamishinan ayyuka da na raya karkara.
Sanarwar rantsarwar ta fito ne daga bakin mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga.
Comments
Post a Comment