Dan majalisar jiha na Gwale ya koma NDC bayan rasa tikitin takara a APC
Ɗan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar mazaɓar Gwale, Abdulmajid Mai Rigar Fata, ya fice daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC).
Tsohon gwamnan Kano kuma jagoran NDC, Rabiu Musa Kwankwaso ne ya tarɓe shi a gidansa da ke Maitama a Abuja ranar Alhamis.
Mai taimaka wa Kwankwaso kan yaɗa labarai, Saifullahi Hassan, ya bayyana hakan ta shafinsa na Facebook, inda ya ce tare da Mai Rigar Fata akwai tsohon mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Gwale, Kabiru Sani Auwal Obi, da Mahadi Isa Umar, waɗanda suma suka shiga NDC.
Rahotanni sun ce Mai Rigar Fata ya sauya sheƙa ne bayan ya kasa samun tikitin APC domin sake tsayawa takarar kujerarsa a zaɓen gaba.
Kafin haka, an zaɓe shi ɗan majalisa a 2023 ƙarƙashin jam’iyyar NNPP, kafin daga bisani ya koma APC tare da gwamna Abba Kabir Yusuf.
Sauyin shekar ya zo ne bayan wata kotun tarayya ta buɗe ƙofa ga ’yan siyasa masu son komawa wasu jam’iyyu domin tsayawa takara a zaɓe mai zuwa.
Jam’iyyar ADC ta ce hukuncin kotun na iya jawo yawaitar ficewar ’yan siyasa daga APC zuwa wasu jam’iyyu.
Comments
Post a Comment