Yanbindiga sun kai hari garin Lakwaya a Kano inda su ka kashe mutane biyu

‘Yanbindiga sun kai hari garin Lakwaya a Kano inda su ka kashe mutane biyu



Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari kauyen Lakwaya da ke ƙaramar hukumar Gwarzo a jihar Kano a ranar Alhamis, inda suka kashe mutane biyu tare da sace shanun jama’a.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun shiga yankin tun wajen karfe 4:00 na yamma a kan babura sama da 30, kuma suka dade suna kai hare-hare kafin jami’an tsaro su isa yankin.

Wani mai rike da mukamin sarautar gargajiya da ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa Daily Nigerian cewa, maharan sun shigo ne ta bangaren Dayi zuwa hanyar Dansarai daga jihar Katsina.

“Yanzu haka ana fafatawa da su, sojoji sun iso yanzu haka, kuma ina tsaye a kan gawar daya daga cikin wadanda aka kashe,” in ji majiyar.

Majiyar ta kara da cewa mutane biyu ne aka tabbatar sun mutu, daya dan kauyen Lakwaya ne, dayan kuma dan Katsina State ne, yayin da wasu da dama suka jikkata.

“Zuwa yanzu ba mu ji cewa sun sace wani mutum ba, amma sun tafi da shanun jama’a,” ya kara da cewa.

Ya ce an kai daya daga cikin gawarwakin zuwa asibitin Gwarzo.

Comments

Popular posts from this blog

Zazzau Emir’s Defamation Case: Court Bars Claimant Over Non-Compliance, Adjourns Proceedings

Alleged 419 Case: Senator Abdu Kwari in Fresh Court Battle Over Property Deal

Maradin, Dan Saran and Wakilin Watsa Labaran Zazzau Honour Loyal Aides with Traditional Titles